Tawagar Falconets ta Najeriya za ta kara da Australia da Mexico a wasannin sada zumunta gabanin gasar cin kofin duniya na mata ‘yan kasa da shekaru 20 na 2024.
Kungiyar Falconets ta fara shirye-shiryen tunkarar gasar ne a Abuja makonni biyu da suka gabata.
Ana sa ran za su je Colombia a wata mai zuwa domin shirin karshe na shirye-shiryensu.
Za a buga wasannin sada zumunta biyu ne a Colombia.
Yanzu haka ‘yan wasa 32 ne ke neman gurbin shiga kungiyar.
A zagayen farko na gasar an hada Falconets ne da Jamus da Venezuela da kuma Korea mai rike da kofin sau uku


