Wasu mutanen da suka tsere daga arewacin Gaza bayan da sojojin Isra’ila suka ce su fice yanzu suna komawa, in ji shugaban hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Falasɗinawa na Majalisar Dinkin Duniya.
Thomas White na hukumar UNRWA ya shaida wa BBC 4 cewa: “Akwai matukar haɗari a arewa amma har a kudancin ƙasar mutane na rasa rayukansu.”
White ya ce mutane 8,000 ne ke samun matsuguni a rukunin gidajen ajiyar kaya na hukumarsa kuma suna rayuwa kan lita ɗaya na ruwa da buredi a rana.
Sojojin Isra’ila sun ce sun kai hari kan wurare 320 a faɗin zirin Gaza cikin sa’o’i 24 da suka wuce