Falasɗinawa sama da rabin miliyan za su koma gidajensu a arewacin Gaza a yau Talata.
Ƙungiyar Hamas ta ce sama da Falasɗinawa dubu 300 waɗanda yaƙi ya tarwatsa sun koma gidajensu da aka yi raga-raga da su a arewacin Gaza a ranar Litinin.
Hotunan da aka gani a yau sun nuna yadda Falasɗinawan ke tafiya a cikin motoci suna ratsa yankunan da aka yi wa rugu-rugu, sannan har yanzu akwai waɗanda suke taka sayyada a ƙoƙarinsu na komawa gida.
Ƙungiyar Islamic Jihad ta saki bidiyon da ke nuna cewa ɗaya daga cikin waɗanda za a saki, Abel Yehud, na nan a raye, wadda ake taƙaddama kan sakin ta tsakanin ɓangarorin biyu.
Isra’ila ta ce ta tabbatar cewa takwas daga cikin waɗanda aka tsara cewa Hamas za ta saki ƙarƙashin yarjejeinyar tsagaita wuta, sun mutu.