Hukumomin Isra’ila za su saki Falasɗinawa ɗari shida da biyu ne a musayar ‘yan ƙasarta shida da Hamas za ta saki a yau Asabar.
Tuni Hamas ta riga ta saki biyar daga cikin ‘yan Isra’ila shida da za ta saki a yau ɗin cikin waɗanda ta yi garkuwa da su.
Ɗan Isra’ila cikon na shida da Hamas ɗin za ta saki nan gaba a yau shi ne Hisham al-Sayed, wanda za a saki ba tare da wani taron jama’a ba, kamar yadda bayanai suka nuna.
Hamas ta kama shi ne tun shekara ta 2015 bayan da ya shiga yankin Gaza.
Rahotanni na nuna cewa tuni Red Cross ta danƙa wa rundunar sojin Isra’ila wasu daga cikin Yahudawan da aka saki yau, kuma sun shiga yankin Isra’ila.
Falasɗinawan da Isra’ila za ta saki 602 a yau, na daga matakin farko na yarjejeniyar dakatar da wuta, wadda ta tanadi cewa Isra’ila za ta saki Falasɗinawa fursunoni da waɗanda take tsare da su 1,900 a musaya da ‘yan Isra’ila 33 da Hamas ta yi garkuwa da su.
An saki sama da Falasɗinawa fursunoni 1,000 da Isra’ila take tsare da su, tun bayan da aka fara aiwatar da kashin farko na yarjejeniyar mai mataki uku, daga ranar 19 ga watan Janairun 2025.
Hukumomin Falasɗinu sun ce a makon da ya gabata Isra’ila ta saki fursunoni Falasɗinawa 369 – kuma 36 daga cikinsu na zaman ɗaurin rai da rai ne sannan ana tsare da 333 ba tare da wata tuhuma ba.
Yawancin Falasɗinawan da ta saki an kai su Gaza wasu an sake su ne a Gaɓar Yamma sannan galibin masu hukuncin ɗaurin rai da rai an fitar da su ne zuwa Masar.
Tun bayan harin ba-zata da Hamas ta kai wa Isra’ila a 2023, yawan Falasɗinawan da Isra’ila ke tsare da su ya ninka biyu zuwa wajen 10,000