Fitaccen lauyan nan mai kare haƙƙin bil adama, Femi Falana ya caccaki manufofin tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu inda ya ce “manufofin masu tsauri” sun shafe masu matsakaicin samu tare da ƙara jefa miliyoyin mutanen ƙasar cikin talauci.
Falana ya ce duk da cewa a baya-bayan nan shugaban ƙasar ya fito ya bayyana cewa ya san irin halin ƙunci da ƴan Najeriya ke ciki, manufofinsa sun ƙara talauta al’umma.
Lauyan mai muƙamin SAN ya shaida hakan ne a hirar da ya yi a gidan Talabijin na Channels inda kuma ya ga baiken yadda gwamnati ke cefanar da kamfanoni ga ƴan kasuwa lamarin da a cewarsa ya ci karo da ƙoƙarin da ake na magance bambancin samu a tsakanin ƴan Najeriya.
Ya ƙara da cewa ya zama dole gwamnati ta sake nazari kan manufofinta tare da samar da tallafi ga ƴan Najeriya masu rauni musamman waɗanda suke yankunan karkara.
Lauyan ya bayyana cewa galibin ƴan Najeriya a yanzu ba sa iya cin abinci sau uku a rana.
“Dole gwamnati ta sake yin nazari kan waɗannan manufofin musamman waɗanda Bankin Duniya da Asusun ba da lamuni na duniya suka bijiro da su, domin ci gaban ƴan Najeriya. Ya kamata gwamnati ta sake nazarin waɗannan manufofin ba tare da ɓata lokaci ba.” in ji shi.
Tun bayan da ya hau karagar mulki a Mayun 2023, Tinubu ya sanar da wasu manufofin tattalin arziki ciki har da cire tallafin mai da barin kasuwa ta tsaida farashin naira.
Janye tallafin man dai ya janyo hauhawar farashin man abin da ya ƙara ta’azzara yanayin talauci da kuma ƙaruwar farashin sufuri har ma da hauhawar farashin kayan masarufi.