Fadar shugaban kasa ta taya Super Eagles murnar samun tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON, wasan kusa da na karshe.
Mai bawa shugaban kasa Bola Tinubu shawara na musamman kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan ta hanyar shafin X.
Onanuga ya taya Ademola Lookman murnar zura kwallo a raga da kuma Victor Osimhen saboda ci gaba da tsoratar da tsaron Angola.
A cewar Onanuga: “Ina taya Super Eagles murnar samun tikitin shiga gasar cin kofin AFCON 2023, da muhimmiyar kwallo da Ademola Lookman ya ci.
“Nijeriya, wacce ta samu gurbin zuwa karo na 16, yanzu ta kai tarihin Masar na yawan wasannin kusa da na karshe.
“Taya murna ga Moses Simon, wanda ya ba da taimakon Lookman kuma ya zama gwarzon dan wasa.
“Ina taya Victor Osimhen murna saboda ci gaba da ruguza tsaron Angola. Manufofin za su zo, a tabbata. “