Fadar Shugaban kasa ta bayyana a matsayin abin bakin ciki da rashin jin dadi, lamarin harbin da ya faru a kusa da Dutsinma a Jihar Katsina, a kan ayarin motocin da ke dauke da jami’an tsaro na Advance Team of Guards, Protocol da kuma jami’an yada labarai gabanin tafiyar Shugaba Buhari zuwa Daura domin yin Sallah.
Malam Garba Shehu, mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa ranar Talata a Abuja. A cewar Malam Garba Shehu.
Ya ce, maharan sun bude wa ayarin motocin wuta ne daga inda suka yi musu kwanton bauna amma sojoji da ‘yan sanda da jami’an ma’aikatar harkokin wajen kasar da ke tare da ayarin sun dakile.
“Mutane biyu da ke cikin ayarin motocin suna karbar magani kan kananan raunukan da suka samu.
“Dukkanin sauran ma’aikata, ma’aikata da ababan hawa sun isa Daura lafiya,” in ji shi.