Fadar shugaban kasa, ta mayar wa tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso martani kan ikirarinsa na cewa gwamnatin Bola Tinubu na nuna bambanci tsakanin yankunan ƙasar.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan sadarwa, Sunday Dare ya fitar a yau Juma’a, ya ce, tun bayan hawan sa mulki, shugaba Tinubu ya gudanar da muhimman ayyuka da dama a Arewacin ƙasar da suka shafi harkoki daban-daban.
Ya bayar da misali da wasu ayyuka fiye da arba’in da ya ce gwamnatin Tinubu ta aiwatar, ko ke aiwatarwa a Arewacin ƙasar daga hawa kan mulki.
Daga cikin manyan ayyukan da ya lissafa akwai gina tituna da bangaren noma da bangaren lafiya da ayyukan ɓaagren makamashi da dai sauransu.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso dai ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da nuna wariya ga Arewacin Najeriya ta hanyar mayar da yawancin albarkatun ƙasar zuwa Kudancin ƙasar.
A wani taron masu ruwa da tsaki na jihar Kano da ya gudana a ranar Alhamis, Kwankwaso ya ce “Bayanai da muka samu na nuna cewa kamar rabin kasafin kuɗi na tafiya zuwa wani ɓangare guda a ƙasar nan,” in ji Kwankwaso.
Kwankwaso wanda ya yi wa jam’iyyar NNPP takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ya zargi jam’iyyar APC da karkatar da albarkatun ƙasa tsakanin ɓangarori biyu na Najeriya.