A yau ne fadar shugaban ƙasa za ta yi wani taron gaggawa tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin malamai da ma’aikatan jami’o’i ASUU.
Za a yi wannan taro ne a yunƙurin kawo ƙarshen yajin aikin jami’o’i da suka tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.
Farfesa Ibrahim Gambari, shugaban ma’aikata na fadar shugaban ƙasa ne zai jagoranci taron, wanda ake sa ran shugabannin addinai za su halarci.taron a yau Laraba.