Fadar shugaban kasa ta taya zababben gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo murna.
Ododo, wanda shine dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya doke abokan takararsa na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) Muri Ajaka, da Dino Melaye na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Jami’in zabe na hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Johnson Urama, ya bayyana Ododo a matsayin wanda ya lashe zaben ranar Lahadi.
“Ahmed Usman Ododo na APC, bayan ya cika sharuddan doka, an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara kuma aka dawo zabe,” in ji shi.
Ododo ya samu kuri’u 446,237, inda ya zarce na kusa da abokin hamayyarsa, Murtala Ajaka na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), wanda ya samu kuri’u 259,052.
Da yake mayar da martani, mai baiwa shugaban kasa Bola Tinubu shawara kan yada labarai da dabaru ya buga akan X: “Ina taya dan takarar APC Usman Ododo murnar lashe zaben gwamnan Kogi.
“Ya doke abokin hamayyarsa, dan takarar jam’iyyar SDP Muri Ajaka da kuri’u sama da 187,000.”