Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa a shirye take tsaf, domin washe ƴan Najeriya da ke son barin kasar Ukraine bayan Rasha ta kutsa ƙasar.
A wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ta hannun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, ta ce, ta yi mamaki kan harin da Rasha ta kai ƙasar.
Wata mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, Francisca Omayuli, ta bayyana cewa, ofishin jakadancin Najeriya a Ukraine ya tabbatar mata da cewa, ƴan Najeriya da ke Ukraine za su kasance cikin tsaro kuma a na ɗaukar matakai na kwashe waɗanda suke so su bar ƙasar.