Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, ta tabbatar da cewa mutane biyu sun samu raunuka tare da yin awon gaba da shanu 16 a unguwar Takazza da ke karamar hukumar Guri ta jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa, Emmanuel Ekot Effiom, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ofishinsa a ranar Talata.
Ya ce, lamarin da ya faru a karshen makon da ya gabata a wani harin ramuwar gayya ne tsakanin al’umomin biyu a karamar hukumar Guri.
Kwamishinan ya bayyana cewa, an jikkata mutane biyu, an kuma lalata musu shanu 16, sannan an lalata wasu siloli a harin.
Ya ce an shirya sintiri na ‘yan sanda a yankin domin kwantar da hankulan lamarin inda suka yi nasarar cafke wasu mutane biyu tare da kwato shanu 11 da aka sace.
“’Yan sanda sun kama wasu mutane biyu da suka je sayar da sassan shanun a kasuwar Maigatari,” in ji shi.
Effiom ya ce ‘yan sanda suna bakin kokarinsu wajen ganin an kama sauran wadanda ake zargin tare da kwato sauran shanun da aka sace daga cikin al’umma.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa al’ummar Takazza sun dawo daidai da yadda aka baza jami’an tsaro a yankunan da abin ya shafa.