Kwamishinan gidaje na jihar Ribas, Gift Worlu ya mika takardar murabus daga gwamnatin gwamna Sim Fubara.
Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 15 ga watan Mayu kuma aka mika wa gwamnan, ta ofishin sakataren gwamnatin jihar.
Worlu shi ne kwamishina na biyu da ya yi murabus daga majalisar ministocin jihar a yau.
Hakazalika, Kwamishinan Ilimi na Ribas, Farfesa Prince Chinedu Mmom a ranar Laraba ya yi murabus daga mukaminsa na mamba a majalisar zartarwa ta jihar.