fidelitybank

Fada tsakanin El-Rufa’i da Uba Sani magajinsa waye mai gaskiya?

Date:

Wani rikici irin na siyasa ya hudo kai a jihar Kaduna da ke tsakiyar Najeriya, bayan da Gwamnan Jihar Uba Sani ya ce gwamnatinsa ba za ta iya biyan ma’aikata albashi ba saboda gagarumin bashin da ya gada daga Malam Nasir El-Rufa’i

Yayin wani taro da ya gudana a ranar Asabar a Kaduna, Uba Sani ya ce ya gaji bashin dala miliyan 587 kwatankwacin naira biliyan 85 ga kuma kudin kamfanonin ‘yan kwangila 115.

Ya ce an cire biliyan bakwai cikin 10 na kason da gwamnatin tarayya ta bai wa Kaduna a watan Maris biliyan bakwai ta tafi a biyan bashi.

Inda ya ara da cewa abin da ya yi wa jihar saura shi ne biliyan uku, ita kuma jihar tana biyan albashin biliyan 5.2 ne duk wata.

Ya ce tashin canjin kudi ya sanya jihar na biyan ninki uku na bashin da aka ci a baya.

“Duk da bashin da mukatarar da ya yi mana kanta, amma gwamnatina ba ta aro ko kobo ba a cikin watanni 9 di muka kwashe muna shugabanci

WaÉ—annan kalamai dai sun janyo martani daga ‘yan siyasar ciki da wajen jihar, kuma cikin waÉ—anda suka yi martanin har da É—an El-rufa’i Bashir.

Bashir El-Rufa’i ya rubuta a shafinsa na X cewa gwamna Uba Sani na neman fakewa da bashin ne ya rufe gazawa da kasawar gwamnatinsa.

Bashir ya yi ikirarin cewa gwamnan na neman sauka daga kai ayyukan da aka zaɓe shi a kai ya manta da aikin da ke gabansa,

“Wadannan sun tabbatar da cewa ba su cancanci wannan mulkin ba baki É—aya kuma hanya guda da za su boye hakan shi ne dauke hankalin mutane. Daga gwamnan da ya tare a Abuja ko da yaushe ya ke barci zuwa muÆ™arrabansa da aka naÉ—a muÆ™amai saboda dalilan siyasa na shiririta,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.

Wannan dambarwa ta sanya mutane tunanin ko an sa zare ne tsakanin gwamna mai ci da wanda ya gaba? In ji BBC.

sahara hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp