Kamfanin Meta wanda ya mallaki dandalin sada zumunta na Facebook da Instagram zai kyale wasu masu amfani da kafofin sadarwan a wasu kasashe su yi kiraye-kirayen daukar matakan raunata Shugaban Rasha Vladimir Putin.
Meta ya ce ya shirya kyale wasu kalaman batanci da na tayar da hankali kamar “A kashe Rashawa masu mamaya”, wadanda a zahiri sun taka tsarin aikinsu.
Sai dai kamfanin ya ce ba zai bari a rika kiraye-kirayen illata fararen hula ‘yan Rasha ba.
A martanin da ta mayar, Rasha ta bukaci Amurka ta taka ma kamfanin birki kan abin da ta kira “matakan cin zarafi” da ya ke son dauka kan Rashar.
Wannan matakin ya biyo bayan wasikun imel da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce ya gani da ke bayyana wannan aniyar ta kamfanin Meta.
A karkashin sabon tsarin, masu amfani da shafukan Facebook da Instagram a rasha da Ukraine da Poland na iya yin kiran a kashe Shugabn Rasha Vladimir Putin da Shugaba Lukashenko na Belarus. in ji BBC.