Kamfanin Meta ya sanar da cewa zai janye dakatarwar da ya yi wa tsohon shugaban Amurka Donald Trump daga shafukansa na Facebook da Instagram.
Shekaru biyu kenan da ya dakatar da Trump, bayan da ya wallafa sakon jinjina ga mutanen da suka yi kutse a majalisa a Washington.
Trump na da mabiya miliyan 34 a Facebook, kuma a ‘yan makonnin da suka wuce mabiyan sun riÆ™a kira da a buÉ—e ma gwanin na su shafinsa.
Shugaban Meta Nick Clegg ya ce a bitar da suka yi sun gano cewa shafin na Trump ba shi da wani hadari a yanzu ga al’umma.