Kamfanin Meta ya sanar da goge shafuka 63,000 na ƴan Najeriya da ke damfarar mutane ta hanyar fakewa da soyayya da kuma maula.
Meta da ke da mallakin Facebook da WhatsApp da Instagram ya ce galibi waɗanda suka fi faɗawa tarkon ƴan damfarar – maza ne a Amurka.
Sanarwar kamfanin ta ce, shafukan da aka goge sun ƙunshi 2,500 na gungun mutane 20.
“Sun fi yaudarar maza a Amurka, kuma suna amfani da shafin bogi,” in ji sanarwar.
Kamfanin ya ƙara da cewa mazambatan kan yi barazanar fallasa hotunan batsa na waɗanda suke son yaudara idan har suka ƙi ba su kuɗin da suka nema bayan musayar hotuna da suka yi tsakaninsu na tsawon lokaci.
Najeriya dai ta yi ƙaurin suna kan harakar zamba a intanet waɗanda ake kira “ƴan yahoo”
Kamfanin ya ce sabbin fasahohin da aka samar ne suka taimaka masa gano mazambatan.
Ana ganin matsalar matsin rayuwa da ake fuskanta a Najeriya ta sa ayyukan zamba a intanet sun ƙaru, galibi kuma tsakanin matasa.


