fidelitybank

Faɗa tsakanin iyalai ta kai ga kisa na ƙara ruwa a Kano

Date:

Ana nuna damuwa kan yadda ake samun karuwar faɗa a cikin gida, al’amarin da ke kaiwa ga kisa tsakanin iyali.

Wannan na zuwa ne bayan da a jihohin Katsina da Kano aka samu wasu matasa samari sun kashe matan iyayensu ta hanyar kai musu hari saboda zargin su ne suka saka aka saki iyayensu mata.

Masana lafiyar kwakwalwa na cewa, ba sai mutum ya na da matsalar kwakwalwa ya ke aikata mummunan laifi ba.

Lamari na baya-bayan nan ya faru ne a unguwar Rijiyar Zaki cikin karamar hukumar Ungogo a jihar Kano a karshen mako.

Inda aka zargi wani matashi da caccakawa kishiyar mahaifiyarsa sukundireba, sannan kuma ya shake wata karamar yarinya abin da ya yi sanadin mutuwarsu.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano ya ce, tuni suka kama wanda ake zargin domin gudanar da bincike.

A watanni baya ma a jihar Katsina an samu irin wannan matsala inda ake zargin wani matashi ya kashe wasu makusantansa.

Bayanai na cewa shi dai wanda ake zargi da kashe kishiyar mahaifiyar tasa ya aikata kisan ne saboda zargin da ya yi cewa itace ta yi sanadin da aka kori mahaifiyarsa daga gidansu.

Likitoci irin su Dakta Aminu Shehu Ibrahim kwararren likitan kwakwalwa a asibitin Malam Aminu Kano ya ce, akwai wani bangare na kwakwalwar mutum da ke taka masa birki a duk lokacin da zai aikata wani abu.

Sai dai kuma idan bai kosa ba, to akwai yiwuwar a samu tunzuri na aikata abin da mutum zai yi dana sani.

Bugu-da-kari masanan na ganin watsi da iyaye maza ko mata ke yi da ‘ya’yansu tare da cmuzguna musu, shi ne babban abin da ke ruruta matsalar al’amarin da ke jefa rayuwarsu cikin kunci da damuwa.

Ana danganta wannan batu da samo asali daga fitar iyayensu mata daga gidajen aurensu.

punch newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Jami’ar Bayero ta Kano ta yi sabon shugaba

Farfesa Haruna Musa, ya karɓi ragamar shugabancin jami’ar Bayero...

Gwamnatin Kano ta amince Barau FC ta yi wasa a filin Sani Abacha

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kungiyar kwallon kafa...

Gwamnatin Tinubu na takalar Kwankwaso da fada – Buba Galadima

Jigo a jam'iyyar NNPP, kuma na hannun tsohon gwamnan...

Newcastle United ta dauki dan wasan tsakiya Jacob daga Aston Villa

Newcastle United ta sanar da daukar dan wasan tsakiya...

Hisba ta kama ‘yan Mata 62 da zargin aikata baɗala a Kano

Hukumar Hisbah ta kama mutane 62 kan zargin aikata...

NNPP ta yi tafka magudi a zabencike gurbin Kano – Farouk Lawan

Tsohon dan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya yi zargin...

Dan shugaban kungiyar Boko Haram ya shiga hannu

Hukumomi a ƙasar Chadi sun kama yaron shugaban ƙungiyar...

Daga yau wankin koda a Najeriya ya koma dubu 12 maimakon dubu 50 – Tinubu

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya amince da rage farashin...

An ceto Mutane 25 da syka kife a kwale-kwalen Sokoto

Hukumomi a jihar Sokoto sun ce, sun samu nasarar...

An fara duba rabon gyaran arzikin Najeriya

Shugaban Hukumar rarraba arziƙin ƙasa RMAFC, Mohammed Shehu, ya...

Kwallaye 6 da aka zurawa Santos a raga ta sanya Neymar ya fashe da kuka

Ɗan wasan tawagar Brazil, Neymar ya fice daga cikin...
X whatsapp