Dan wasan Everton Richarlison zai yi jinyar makonni masu yawa sakamakon raunin da ya samu a wasan da Crystal Palace ta doke su da ci 3-1.
An sauya Richarlison ne bayan mintuna 58 na wasan, wanda magoya bayan Everton su ka yi wa kocin Rafael Benitez ihu saboda sauya shi da ya yi.
Amma Benitez ya ce bayan wasan ya cire shi saboda rauni ne.
Wasan Palace kuma ya ga Andros Townsend ya karye ƙafarsa kuma kyaftin din Seamus Coleman ya sami rauni a kashi.
Dan wasan Ingila, Dominic Calvert-Lewin na ci gaba da fama da jinya ttun watan Agusta sakamakon ciwon cinya.
Haka kuma mai tsaron baya Yerry Mina, wanda ya shafe mintuna 31 kacal bayan ya dawo bayan watanni biyu kafin ya sake samu matsala.
A halin yanzu Everton ta na matsayi na 14 a teburin Premier.