Jiragen Rasha na fuskantar rashin hanya kwatakwata a nahiyar Turai wadda ƙungiyar Tarayyar Turai EU, ta sanar da matakin hana wa jiragen bi ta sararin samaniyar ƙasashen ƙungiyar.
Tun farko ƙasashen na Turai ɗaya bayan ɗaya suka ce za su rufe sararin samaniyarsu ga jiragen Rasha, ciki har da Jamus na tsawon wata uku.
Yayin da aka rufe samaniyar Ukraine, yanzu jiragen na da tsirarun hanyoyin da za su iya bi a nahiyar.
Gomman jirage a filayen jirage na Domodedovo da Sheremetyevo sun soke jigila a yau Lahadi, ciki har da na zuwa Paris, Faransa, da Vienna da Kaliningrad.