Gwamnan babban bankin ƙasa, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa, ya gana da shugabannin bankunan kasuwanci 15 na kasar nan.
A cewarsa, ya tattauna da su yadda za a sassauta tabarbarewar kudaden da ake fama da su a kasar nan, biyo bayan umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar a watsa shirye-shiryen sa ga al’ummar kasar a safiyar ranar Alhamis.
Buhari ya ba da umarnin a sake dawo da tsoffin takardun kudi na N200 kuma a amince da su a matsayin takardar doka har zuwa ranar 10 ga Afrilu.
Emefiele ya zanta da manema labarai na fadar shugaban kasa jim kadan bayan halartar taron da Buhari ya yi da kwamitin adhoc na majalisar wakilai a fadar shugaban kasa inda sabon tsarin gyaran naira da tsarin musanya naira ya kasance kan gaba.
Emefiele ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa, za a samar da tsofaffin takardun kudi na Naira 200 nan take.