Wata kungiya mai suna Unified Northern Nigeria Youth Forum, ta ce, gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, shi ne mutum daya tilo da zai iya lashe zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC.
POLITICS NIGERIA ta rawaito cewa, duk da cewa Emefiele ba a san shi a wata jam’iyya ba, kuma bai taba bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya ba, amma wasu kungiyoyi masu goyon baya a fadin kasar na tallata shi.
Mohammed Salisu Danlami, ya bayyana kwanan nan a wani taron manema labarai a Lokoja, Jihar Kogi, cewa Emefiele ya yi fice, don haka ya cancanci ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari.