Dakataccen gwamnan babban bankin (CBN), Godwin Emiefele, ya nemi wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta hana gwamnati da hukumar DSS ci gaba da tuhumar sa kan mallakar makami ba bisa ƙa’ida ba.
Ya kuma nemi kotun ta wanke shi daga duka zarge-zargen da hukumar DSS ke yi masa.
Emefiele wanda kotu ta bayar da belin sa a ranar 25 ga watan Yulin 2023, amma har yanzu hukumomi na ci gaba da tsare shi.
Lauyan Emiefele, Joseph Daudu, wanda ya shigar da buƙatar a madadin wanda ake zargi ya nemi mai shari’a Nicholas Oweibo ya tabbatar da belin dakataccen gwamnan babban bankin da kotu ta bayar tun da farko.
Ya yi fatan kotun ta haramta duk wani yunƙuri na ci gaba da gurfanar da Mista Emiefele har sai an yi biyayya ga hukuncin da kotu ta bayar game da belinsa.