Shugaba Nayib Bukele na El Salvador ya sanar da taron kasashe 44, don tattauna a kan Bitcoin da batutuwa da dama.
Nayib Bukele ya sanar da hakan ta shafinsa na Twitter a daren Lahadi, yana mai cewa taron zai gudana ne a El Salvador.
Sai dai Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sha yin gargadi game da yin ciniki da cryptocurrency tare da ba da umarni ga bankunan da su rufe asusun mutane ko hukumomin da ke hada-hadar cryptocurrency.
Wakilai daga kasashe 44, wadanda suka hada da bankunan tsakiya na 32 da hukumomin kudi na 12, za su hadu a El Salvador don yin magana game da hada-hadar kudi, tattalin arzikin dijital, banki marasa banki da karbe Bitcoin na kasar.
Kasashen sun hada da Najeriya, Masar, Nepal, Pakistan, Bangladesh, Kenya, Namibiya, Uganda, Rwanda, Paraguay, Angola, Guinea, Madagascar, Jamhuriyar Dominican, da dai sauransu. A cewar Daily Trust.