fidelitybank

El-Rufa’i ya kai wa tsohon Hadiminsa ziyara a gidan Birsin

Date:

Tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya ziyarci tsohon shugaban fadar gwamnatin Kaduna wanda babban amininsa ne da ke tsare a gidan gyara hali dake Kaduna.

Jami’an tsaro sun kama Bashir Saidu Tsohon Hadimin El-Rufa’i a Kaduna ranar Laraba, bisa zargin wai ya yi sama da faɗi da kuɗaɗen jihar lokacin mulkin El-Rufa’i.

Ko da ya ke duk da musanta wannan zarge-zarge da ake masa a kotun Rigasa da ya yi, alkalin Kotun ya hana shi beli yayin da ya yanke masa hukunci zaman gidan kaso na makonni uku.

Rahotanni sun nuna cewa El-Rufai tare da wasu tsoffin kwamishinoninsa, Hafsat Baba,Jaafaru Sani, da Ibrahim Hussaini ne suka ziyarci Saidu a kurkukun.

El-Rufa’i ya shafe mintuna 30 yayin zayarar.

Da yawa daga cikin masu fashin baki a harkar siyasar Kaduna, sun yi tir da wannan kamu da aka yiwa Bashir Saidu, inda suka alaƙanta shi da bibiyar da gwamnatin Kaduna ke yi wa tsoffin na kusa da tsohon gwamnan, El-Rufa’i.

Tun bayan ɗarewarsa gwamnatin Kaduna, Uba Sani ya zargi gwamnatin El-Rufai da handame wasu kuɗaɗen da gwamnatin ta ciwo bashi da sunan yin ayyukan raya kasa.

Wannan zargi ya sa an raba jiha tsakanin magoya bayan yan siyasan.

Lamarin na cigaba da kazanta a halin yanzu inda gwamnatin Uba Sani ta lashi takobin sai ta bankaɗo kamayamayar da aka yi a karkashi gwamnatin El-Rufai da wasu ke ganin da shi a dama a wancan lokaci.

nnn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...

Sarkin Kano na 15 ya dakatar da yin hawan Sallah

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado...

Maniyacin jihar Kano da yake kokarin zama Alhaji ya rasu a Saudiyya

Daya daga cikin alhazan jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, an...

Tinubu ya bayar da tallafin Biliyan Biyu da Tirela 20 na Shinkafa ga al’ummar Mokwa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce, shugaban ƙasar...

Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya kai ziyara ga...

An samu gawar mutane 7 a ambaliyar Neja

Rahotonni na cewa masu aikin ceto sun zaƙulo gawar...
X whatsapp