Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya janye daga kujerar minista a gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu, inji rahoton Premium Times.
Har ila yau, tsohon gwamnan ya ba da shawarar a maye gurbinsa da wani.
Jaridar ta yanar gizo ta nakalto majiyar fadar shugaban kasa ta ce, El-Rufai ya sanar da shugaba Tinubu cewa, ba zai sake la’akari da nadin da ya yi masa a matsayin minista a gwamnati ba.
Rahotanni sun bayyana cewa El-Rufai ya tabbatar wa Tinubu cewa zai ci gaba da bayar da gudummawar kason sa don ci gaban kasa a matsayinsa na dan kasa mai zaman kansa.
Rahoton ya ce El-Rufai ya shawarci Jafaru Ibrahim Sani, wanda ya rike mukamin kwamishina a ma’aikatu uku – Ilimin Kananan Hukumomi da Muhalli a Jihar Kaduna a matsayin wanda zai maye gurbinsa.
Majalisar dattawan ta samu jinkiri wajen tabbatar da El-Rufai da wasu ministoci guda biyu saboda rashin tsaro.
Majalisar dattijai ta mika sunayen mutane 45 ga shugaban kasa.