fidelitybank

El-Rufa’i da tawagarsa su sani cewa ni ne ɗan takarar shugaban ƙasa a SDP – Adewole

Date:

Jagoran jam’iyyar SDP na ƙasa, kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar jam’iyyar a zaɓen 2023, Adewole Adebayo ya ce duk wanda ya shiga jam’iyyar tasu, yana sane da aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugabancin ƙasar, kamar yadda ƴan jam’iyyar suka riga suka sani.

Cikin wata hira da gidan talbijin na Arise TV, Mista Adebayo yana da ƙwarin gwiwar sake yi wa jam’iyyarsa takara a zaɓen 2027, duk kuwa da irin manyan ƴan siyasar da ake sa ran za su koma jam’iyyar.

Ɗan siyasar ya ce ba ya fargabar rasa takara, duk kuwa da samun sabbin ƴan siyasar da ke shiga jam’iyyar daga wasu jam’iyyun.

“Ai duk mutumin da yake ganin shigowar wasu jam’iyyarsa zai zame masa barazana, ba zai iya zama shugaban Najeriya ba.”

“Ku fahimci wani abu, ba na damuwa da waɗanda ke shigowa jam’iyyarmu, duk wanda ya shigo yana sane cewa ni ne zan yi wa jam’iyyar takara a 2027”, kamar yadda ya bayyana a hirar.

Kalaman na Mista Adewole na zuwa ne kwanaki bayan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya koma jam’iyyar ta SDP bayan ficewa daga APC.

Jagoran SDPn ya kuma yaba wa El-Rufai bisa kasancewarsa jigo a siyasar Najeriya.

naija news legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp