fidelitybank

El-Rufa’i da abokan hamayya sun buƙaci Majalisa ta yi watsi da dokar ta ɓaci a jihar Rivers

Date:

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El Rufai da ɗantakarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin jam’iyyar Labour, Peter Obi sun yi fatali da matakin Shugaban ƙasa na ƙaƙaba dokar ta-ɓaci a jihar Rivers.

El Rufai da sauran jagororin jam’iyyun hamayya sun buƙaci Majalisar dokokin Najeriya ta yi watsi da ƙudirin.

A ranar Talata ne Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers inda ya dakatar da Gwamna Siiminalayi Fubara da mataimakiyarsa da mambobin majalisar dokokin jihar.

Shi ma ɗantakarar shugaban ƙasa a 2023 ƙarkashin inuwar PDP, Atiku Abubakar, a jawabin a ya yi ranar Alhamis, ya zargi Tinubu da nuna ɓangaranci.

Atiku Abubakar ya kuma nemi Shugaba Tinubu da ya janye matakin wanda ba ya bisa kundin tsarin mulkin ƙasa sannan ya maido da zaɓaɓɓn gwamna da mataimakiyarsa da sauran mutanen da aka dakatar kan kujerarsu.

A cewarsa sun yi tur da matakin sannan sun yi kira ga ƴan Najeriya da su soki ƙudirin wanda ya saɓawa kundin tsarin mulkin ƙasar da kuma dimokraɗiyya.

assu news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...

Sarkin Kano na 15 ya dakatar da yin hawan Sallah

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado...

Maniyacin jihar Kano da yake kokarin zama Alhaji ya rasu a Saudiyya

Daya daga cikin alhazan jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, an...

Tinubu ya bayar da tallafin Biliyan Biyu da Tirela 20 na Shinkafa ga al’ummar Mokwa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce, shugaban ƙasar...

Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya kai ziyara ga...

An samu gawar mutane 7 a ambaliyar Neja

Rahotonni na cewa masu aikin ceto sun zaƙulo gawar...
X whatsapp