Kungiyar El-Kanemi Warriors ta kammala daukar Gabriel Wassa daga Plateau United.
Wassa ya shafe kakar wasan bara a matsayin aro a kungiyar kwararrun kwallon kafa ta Najeriya, Niger Tornadoes.
Dan wasan mai shekaru 26 yana daya daga cikin mafi kyawun masu tsaron baya a cikin NPFL.
Dan wasan baya yana da gogewa sosai bayan ya buga wasa a manyan kungiyoyi a Najeriya da suka hada da Rivers United da Lobi Stars da Akwa United.
Ya buga wasanni 17 a kungiyar Niger Tornadoes a kakar wasan data gabata kuma ya zura kwallo daya.
El-Kanemi ya dawo NPFL bayan ya shafe shekaru a gasar NNL ta Najeriya.