Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya aika wasiƙa ga Kotun Birtaniya da ta samu tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ike Ekweremadu da mai ɗakinsa Beatrice da laifin safarar ɗan’adam don cirar sashen jikinsa.
A wasiƙar da ya aike wa babban akawun kotun da ke London, tsohon shugaban ƙasar ya nemi akawun ya sa baki, kuma ya tabbatar cewa gwamnatin Birtaniya ta yi sassauci a hukuncin da za ta yanke.
Manyan jaridun Najeriya sun ruwaito cewa Obasanjo ya aika wasiƙar Birtaniya, inda Ekweremadu ke iya fuskantar ɗaurin shekara 10 bisa tanadin dokokin ƙasar, bayan an same shi da laifi.
Tun bayan samun Ekweremadu da mai ɗakinsa da laifin ne, ake tsare da su har zuwa 5 ga watan Mayu – ranar da za a yanke hukunci.
An kama Ekweremadu da matarsa bayan wani matashi ya yi ƙorafi kan yadda mutanen biyu ke ƙoƙarin cire masa ƙodarsa.
Sai dai, Obasanjo a cikin wasiƙar mai kwanan watan 3 ga Afrilun bana, ya ce Ekweremadu da mai ɗakinsa sun koyi darasi daga abin da ya faru.