fidelitybank

Ekiti da Osun: APGA ta fara sayar da fom din takarar Gwamna

Date:

Jam’iyyar APGA za ta gudanar da zabukan fitar da gwani na gwamna a jihohin Ekiti da Osun a ranakun 27 ga watan Janairu da 10 ga watan Maris.

A cikin wani jadawalin ayyuka na wucin gadi wanda Sakataren kungiyar, APGA na kasa, Mista Ifeanyi Mbaeri, ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta ce za a samu fom din  nuna sha’awa a kan kudi Naira miliyan 2, yayin da za a sayar da fom din tsayawa takara a kan Naira miliyan 10.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Bisa ikonta a karkashin sashi na 12 (3) da na 24 na kundin tsarin mulkin jam’iyyar APGA na 2019, da kuma bin jadawalin INEC da jadawalin ayyukan zaben gwamnonin jihohin Ekiti da Osun na 2022, kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na Jam’iyyar (APGA) ta amince da jadawalin gudanar da zaben fidda gwani na gwamnonin jihohin Ekiti da Osun a 2022.

“Za a gudanar da zaben fidda gwani na jihar Ekiti a ranar 27 ga Janairu, 2022, yayin da zaben firamare na jihar na musamman zai gudana a Osogbo, jihar Osun a ranar 10 ga Maris, 2022.”

APGA ta ce masu neman takarar bangaren mata da masu fama da nakasa su biya kashi 50 cikin 100 kawai na kudaden da aka tanada na duka fom na nuna sha’awa da na takara.

Karkashin jadawalin da a ka amince da zaben fidda gwani na Ekiti, za a gudanar da siyar da fom na nuna sha’awa da na takara a sakatariyar jam’iyyar APGA ta kasa da ke Abuja tsakanin 20 ga Disamba zuwa 10 ga watan Janairu, 2022.

A ranar 28 ga watan Junairu ne za a yi shawarwarin daukaka kara/hukumomin da suka taso daga zaben fidda gwani na Ekiti.

breaking news in nigeria today punch

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp