Ekerette Udom na shirin kammala komawa Al Najaf a gasar lig din kasar Iraqi kan kudin da ba a bayyana ba.
Udom ya bar kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Sunshine Stars domin tafiya kasar waje.
An hange dan wasan mai shekaru 20 tare da wakilinsa a lokacin da ya isa don kammala yarjejeniyar.
A cewar rahotanni, babban mai tsaron baya ya kasance abin sha’awa daga Rivers United bayan tafiyar Dennis Ndassi.
An fahimci Udom ya ki amincewa da ingantaccen kwangilar ci gaba da zama a Owena Waves.
Ya taka rawar gani a dukkan wasannin Sunshine Stars a gasar NPFL a kakar wasan data gabata sannan kuma ya wakilci tawagar ‘yan kasa da shekaru 20 ta Najeriya.
Udom ya koma kungiyar Edith Agoye daga Dakkada FC a kakar 2022-23 NPFL.


