fidelitybank

EFCC ta ƙwace unguwar da wani tsohon jami’in gwamnati ya mallaka a Abuja

Date:

Hukumar EFCC ta samu nasarar ƙwace kadara mafi girma a tarihinta, inda a ranar Litinin, 2 ga watan Disamban 2024, mai shari’a Jude Onwuegbuzie ya mallaka wa gwamnati wani rukunin gidaje, wanda aka gina a fili mai mai faɗin murabba’in ƙasa 150,500, mai ɗauke da rukunin gidaje 753 da wasu gine-ginen a Abuja.

Wannan shi ne ƙwace kadara mafi girma tun bayan kafa hukumar EFCC a shekarar 2003.

Kotu ta ƙwace rukunin gidajen ne mai lamba 109 a yankin Zone C09 da ke unguwar Lokogoma a Abuja, wanda kotun ta ce ta mallakin wani tsohon jami’in gwamnati ne, kamar yadda wata sanarwa da EFCC ta fitar ta nuna.

Da yake hukunci kan ƙwace rukunin gidajen, mai sharii’a Onwuegbuzie ya ce wanda ake ƙara ya kasa gamsar da kotun abin da zai hana a ƙwace masa kadarar, “wadda ake zargin ya mallaka da kuɗaɗen da ya samu ta wasu hanyoyi zamba. Don haka an ƙwace kadarar, an kuma miƙa ga gwamnatin tarayya.”

Tun da farko, a ranar 1 ga watan Nuwamban 2024 ne kotun ta fara ƙwace rukunin gidajen na wucin-gadi, kafin yanzu ta ƙwace baki ɗaya.

Sanarwar ta ƙara da cewa ana cigaba da binciken jami’in gwamnatin

Shugaban hukumar, Mr Ola Olukoyede, ya sha nanata cewa ƙwace kadarorin da aka mallaka ta hanyoyi marasa kyau na da matuƙar muhimmanci a yaƙi da cin hanci da rashawa.

legit nigeria news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...
X whatsapp