fidelitybank

EFCC ta yi wa kasuwar canji a Abuja ƙawanya

Date:

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta yi wa kasuwar musayar kudaden ketare ta bayan fage dake Zone 4 a Abuja ƙawanya, inda suka tafi da wasu daga cikin ‘yan chanjin.

Wasu da lamarin ya faru akan idon su sun ce jami’an EFCCn sun isa wajen ne da misalin 2:00 na rana, inda suka datse dukkan wata hanya da zata kai layin da ‘yan chanjin suke harkokinsu, wanda hakan ya kawo tsaikon harkoki a kasuwar da ke Zone 4 na tsawon kusan sa’a 2.

Sai dai har yanzu, hukumar ta EFCC bata kai ga cewa uffan ba kan wannan batu.

Hakan na zuwa ne a dai dai lokacin da ake ci gaba da samun tashin farashin dala a kasuwanin bayan fage a Najeriya, wanda masu ruwa da tsaki a harkokin tattalin arzikin kasar ke alakanta shi da matakin da babban bankin kasar ya dauka na sauya fasalin takardun kudin kasar nan da watan Janairun sabuwar shekara mai zuwa ta 2023.

Faruwar wannan lamari dai ya dauki hankalin al’umma musamman masu harkokin musayar kudade a Najeriya na fargabar rashin sanin yadda lamarin ka iya fadada zuwa wasu jihohin kasar.

punch news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Hogan ya mutu bisa cutar gazawar koda

An bayyana cikakkun bayanai game da mutuwar ɗan wasan...

Sojoji sun kashe rikaken dan Bindiga Dan Dari Biyar a Sokoto

Dakarun Operation FANSAR YANMA sun yi nasarar fatattakar wani...

An kashe utane 30 a yakin Thailand da Cambodia

An shiga kwana na uku na faɗan kan iyaka...

Ba mu ƙayyade shekarun shiga ƙaramar sakandare JSS1 – Ma’aikatar Ilimi

Ma'aikatar Ilimi a Najeriya ta musanta rahoton da wasu...

Ido da Ido na ga yadda Sojojin Isra’ila ke kashe Falasdinawa – Tsohon Sojin Amurka

Wani tsohon sojan Amurk ya ce, ya ga yadda...

‘Yan majalisar Birtaniya 220 na neman ƙasar ta amice da ƙasar Falasɗinu

'Yan majalisar Birtaniya 220 sun nemi gwamnatin ƙasar ta...

Buhari yaki karbar kyautar Agogon lu’u-lu’u da jirgin sama – Garba Shehu

Mai magana da yawun tsohon Shugaban Najeriya Muhammad Buhari,...

An kama wanda ya kashe tsohuwar Matarsa a Jigawa

Ƴansandan Jihar Jigawa sun ce, sun kama wani mutum...

Fadar shugaban kasa ta mayar da martani kan Kwankwaso

Fadar shugaban kasa, ta mayar wa tsohon gwamnan Kano...

Barau FC ta naɗa Ladan Bosso sabon kocinta

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC ta sanar da...

Am fara dawo da ‘yan Najeriya daga Afrika ta Tsakiya

Hukumomi a Najeriya sun ce, sun fara ƙoƙarin mayar...

G-Fresh da Hamisu Breaker sun samu gurbi kurkuku bayan sun watsa Naira

Babbar kotun tarayya da ke jihar Kano ɗaure shahararrun...
X whatsapp