Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa a Najeriya, EFCC, ta yi dirar mikiya a gidan tsohon gwamnan jihar Imo, kuma daya daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC mai mulki Rochas Okorocha.
Jaridar Punch ta rawaito cewa jami’an EFCC sun dira gidan Mr Okorocha da ke babban birnin kasar Abuja ranar Talata, sai dai kawo yanzu babu tabbacin abin da ya kai su gidan, amma daya daga cikin tsofaffin masu bai wa Okorocha shawara ya tabbatar wa jaridar tabbas jami’an sun shiga gidan.
Shi ma gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa, jami’an EFCC sun je gidan Rochas da nufin kama shi.
A bidiyon da Channels din ta samu, ya nuna jami’an EFCC suna kai komo a farfajiyar gidan tsohon gwamnan. Sun kafe sai dan takarar shugaban kasa ya fito sun cafke shi, ko kuma ya mutunta tsohon goron gayyatar da hukumar ta aika masa, da ya ki zuwa.
Jami’an sun sanya shinge a hanyar da za ta sada mutum da gidan Okorocha, kamar yadda suka bayyana jami’an EFCC sun ce babu wanda zai fita daga gidan har sai Okorocha ya mika kan shi gare su.
Ba da jimawa ba, aka ga motocinsu na ficewa daga unguwar.