Hukumar Yaƙi da cin Hanci da Rashawa ta Najeriya, EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan Babba Bankin Ƙasar, Godwin Emefiele a gaban kotun kan zargin amincewa da kashe naira biliyan 18.96 wajen buga takardun kuɗi na naira miliyan 684.5.
An gurfanar da tsohon gwamnan ne a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa tuhume-tuhume guda huɗu.
To sai dai mista Emefiele ya musanta duka zarge-zargen da aka tuhume shi a kansu.
Kan haka ne lauyansa ya nemi kotun ta bayar da belinsa, inda aka bayar da belinsa kan naira miliyan 300, da sharaɗin mutum biyu da suka tsaya masa.
Haka kuma kotun ta ce dole ne tsohon gwamnan babban bankin ya gabatar mata takardun biza da fasfonsa, kuma ba zai fice daga ƙasar ba, dole sai da izinin kotun.
Godwin Emefiele ya fuskanci jerin tuhume-tuhume tun bayan da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya dakatar da shi a shekarar da ta gabata kan zargin saɓa ƙa’idan aiki.