fidelitybank

EFCC ta sake gurfanar da ɗan tsohon shugaban PDP a kotu

Date:

Hukumar da ke Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon ƙasa EFCC, ta sake gurfanar da Mamman Ali, ɗa ga tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa Ahmadu Ali, bisa zargin zambar naira biliyan 2.2 na tallafin man fetur.

Kamfanin dillancin labarai NAN, ya ruwaito cewa an sake gurfanar da Mamman Ali tare da wani mutum mai suna Christian Taylor da kamfanin mai na Nasaman Oil Services Ltd a gaban wata kotu a birnin Legas.

An gurfanar da su ne bisa zarge-zagen laifuka 49 ciki har da haɗa baki, da yaudara da zamba cikin aminci, da yin ƙarya domin karɓar kuɗi da amfani da takardun bogi.

To sai dai mutanen sun musanta duka zarge-zargen da ake yi musu.

Lauyan hukumar EFCC Samuel Atteh, ya nemi kotun da ta sanya ranar sauraron ƙarar ta yadda zai gabatar da shaidunsa da za su tabbatar da zargin da hukumar ke yi wa mutanen.

To sai dai lauyan waɗanda ake zargin Kolade Obafemi ya nemi kotun da ta bayar da belin waɗanda yake karewa.

To amma lauyan EFCC ya ce abu mafi muhimmaci kan wannan shari’a shi ne waɗanda ake zargi su riƙa halartar kotun don fuskantar tuhumar da ake yi musu.

Daga ƙarshe alƙalin kotun ya bayar da umarnin cewa waɗanda ake zargin su ci gaba da kasancewa a hannaun hukumar EFCC har zuwa lokacin da za a gabatar da takardun neman belinsu a hukumance.

Alƙalin ya kuma ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 30 ga watan Mayu mai zuwa.

A ɗaya daga cikin zarge-zargen da hukumar EFCC ke yi wa mutanen, shi ne zargin haɗa baki don karɓar naira miliyan 750 daga gwamnatin tarayya, don karyar bai wa kamfanin mai na Nasaman Oil Services Ltd, ƙarƙashin asusun tallafa wa kamfanonin mai don shigo da litar mai 10,031,986, da kamfanin na Nasaman Oil Services Ltd, ya yi iƙirarin cewa ya saya daga kamfanin man Birtaniya na SEATAC Petroleum Ltd.

tribune news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp