Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta mika kadarori 14 da ta kwato ga gwamna Peter Mba na jihar Enugu.
Shugaban Hukumar, Ola Olukoyede, a yayin bikin mika kadarorin da aka gudanar a shalkwatar EFCC dake Jabi, Abuja, a yau, ya bayyana cewa, kadarorin da hukumar ta kwato ta mallakawa gwamnatin tarayya.
Olukoyede ya ci gaba da cewa, hukumar EFCC ta fara gudanar da bincike kan lamarin tun a shekarar 2007.
Ya kuma yi nuni da cewa, shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin mika kadarorin da suka hada da gidaje, na’urorin gidajen rediyo da talabijin, da kayayyakin cibiyoyin kiwon lafiya da dai sauransu, zuwa ga gwamnatin jihar Enugu, biyo bayan bukatar da hukumar EFCC ta yi.