fidelitybank

EFCC ta kwace fasfo din Sadiya da Edu da Halima

Date:

Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa ta karɓe fasfon tafiye-tafiye na ministar jin ƙai da aka dakatar, da kuma na wadda ta gabace ta, wato Sadiya Umar Farouq, waɗanda ake ci gaba da bincike a kansu kan zargin aikata ba daidai ba, da dukiyar al’umma.

Haka kuma, EFCC ta kwace fasfo ɗin Halima Shehu, shugabar hukumar ba da tallafin dogaro da kai NSIPA – wadda ita ma aka dakatar bisa zargin almubazaranci da kuɗin da suka kai naira biliyan 44 da miliyan 800 a ƙarƙashin ma’aikatar jin ƙai,.

EFCC ta ce ta kwato naira biliyan 39.8 cikin biliyan 44.8 da ake zargin Halima ta yi sama da faɗi da su.

A ranar Talata ne, hukumar ta tsare Betta Edu tare da yi mata tambayoyi tsawon kusan awa 10 a Abuja. An yi mata tambaya ne kan kuɗin da suka kai miliyan 585 na hukumar.

A yau Laraba ne ake tsammanin Sadiya da Betta da kuma Halima za su sake gurfana gaban hukumar domin ci gaba da yi musu tambayoyi.

breaking news in nigeria today 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp