Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, a ranar Juma’a, ta kasa shawo kan babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, ta mika karar da ta fara yi wa tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, zuwa Legas domin ci gaba da shari’a.
Kotun, a wani hukunci da mai shari’a Inyang Ekwo, ya yanke, ta ce bukatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta yi, ba ta da wani hakki.
Mai shari’a Ekwo ya bayyana cewa bukatar EFCC, ta yi daidai da cin zarafin tsarin shari’a, yana mai jaddada cewa sashin kotun na Abuja na da hurumin gudanar da shari’ar.