fidelitybank

EFCC ta kama tsohuwar kakakin majalisa da almundahanar miliyoyin Naira

Date:

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta cafke tsohuwar kakakin majalisar wakilai, Patricia Etteh.

Jaridar Guardian ta tattaro a daren jiya cewa, sashen ayyuka na musamman na EFCC na tuhumar Etteh, bisa zarginta da hannu a badakalar samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a jihar Akwa Ibom.

A cewar manyan majiyoyin EFCC, “An kama ta ne kan wata kwangilar Neja-Delta (NDDC) a shekarar 2011. kwangilar aikin samar da hasken rana ne a yankunan karkara na wasu al’ummomi a Akwa Ibom. An bayar da kwangilar ne ga wani kamfani mai suna Philjim Projects Limited

Kudaden kwangilar Naira miliyan 240 ne hukumar NDDC ta bayar a wani bangare na ayyukan ci gaban al’umma. An fara sakin Naira miliyan 34, sai kuma Naira miliyan 253, wanda ya kai Naira miliyan 287 da aka biya.

“Damuwarmu akan wannan lamari shine Etteh ba darakta ba tace kuma ‘yar kwangila ba ce, amma binciken mu ya nuna cewa, ‘yar kwangilar ta biya ta jimillar kudi naira miliyan 130.

“Lokacin da masu bincikenmu suka tunkare ta da wadannan kudade, sai ta ce bashin ne da ta baiwa dan kwangilar da ke gudanar da aikin.

www.punch news.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp