Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta kama wani matashi mai shekaru 38, mai suna Salman Umar Hudu, a Abuja.
An kama Hudu ne a wani otel a ranar Talata bisa zarginsa da yi wa Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar, matashin mai shekaru 38 ya samu N100,000 daga hannun wani da ke fake da cewa shi Bawa ne kuma yana tafiyar da duk wani lamari da hukumar yaki da cin hanci da rashawa.
Karanta Wannan: Akwai tukwici ga duk wanda ya fallasa masu boye sababbin kudi – EFCC
EFCC ta ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu bayan ya bayar da bayanai masu amfani.
Sanarwar ta kara da cewa: “Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, a ranar Talata, 14 ga Fabrairu, 2023, ta kama wani mutum mai suna Salman Umar Hudu, mai shekaru 38, dan asalin Kano, a wani otal da ke Abuja, bisa zarginsa da yin wa kansa karya. Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, Abdulrasheed Bawa, da sauran jami’an Hukumar, tare da karbar Naira 100,000.00 daga hannun mutumin da ya tabbatar da cewa zai iya ‘kamawa’ duk wata matsala da ta shafi EFCC.”