Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, shiyar jihar Gombe, ta kama wani mutum mai suna Zakariya Muhammad, da laifin watsa takardar Naira, al’adar da ake ganin tamkar cin zarafin kudin kasar nan.
Kamen dai ya biyo bayan bayanan sirri da ke alakanta Muhammad da aikata laifin, wanda ya faru a Tunfure dake jihar Gombe.
Hukumar EFCC ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Larabar da ta gabata cewa, an gano Muhammad ne a wani faifan bidiyo inda aka gan shi yana rawa yana watsa ‘yan Naira 200.
A cewar sanarwar, Muhammed ya amince da cewa, shi ne mutumin a cikin faifan bidiyon da aka yi masa tambayoyi.
Sanarwar ta ce, za a gurfanar da shi gaban kotu bayan kammala bincike.
Dokar Babban Bankin kasa (CBN), musamman sashe na 21, ta yi haramta cin zarafin Naira.
Dokar ta tanadi hukuncin daurin akalla watanni shida a gidan ajiya da gyaran hali, ko kuma tarar da ta fara daga Naira 50,000 ga wadanda suka aikata laifin.