Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya (EFCC), ta kama wata mata da katunan zaɓe 18 a jihar Kaduna da kuma wasu a Kano da Abuja.
Jami’an hukumar ne suka kama matar da safiyar yau a unguwar Badarwa da ke Kaduna bayan kai wani samame.
An kuma samu wata takarda ɗauke da jerin sunayen masu zaɓe guda 17 da asusun ajiyarsu na banki da lambobinsu na waya a matsayin waɗanda ke da damar yin zaɓe a mazaɓar Badarwa/Malali 01 da 08 da ke karamar hukumar Kaduna ta Arewa.
An kama ta ne lokacin da jami’an na EFCC suka bad-da-kama, inda suka nuna cewa za su sayar da katunansu na zaɓe.
A halin yanzu dai tana hannun jami’an na EFCC a shiyyar Kaduna, inda suke ƙoƙarin gano wasu mutane da ke tare da ita waɗanda ta ce su ma suna karɓar katunan zaɓen mutane da kuma ba su kuɗi ta amfani da POS da kuma tura kuɗin ta intanet.
A Kano kuma EFCC ta ce, ta kama wani mutum da take zargi da sayen kuri’u, inda suka same shi da tsabar kuɗi naira 194,000 a rumfar zaɓen Gidan Zakka da ke Goron Dutse a karamar hukumar ƙwaryar birnin Kano.
A Abuja kuma hukumar ta ce ta yi nasarar kama wakilin wata jam’iyya yana sayen kuri’u a karamar hukumar Abaji na babban birnin tarayya, ta hanyar tura musu kuɗi ta intanet.