Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) shiyyar Ilorin, sun tsare sama da mutane sittin da daya da ake zargi da damfara ta yanar gizo.
Kamen wanda aka gudanar a wasu ayyuka guda biyu sun hada da wani Raji Wasiu Babatunde wanda hukumar ta kama a shekarar da ta gabata, ta gurfanar da shi a gaban kuliya, aka kuma yanke masa hukunci, amma ya koma amai ya sake kama shi.
A wata sanarwa da hukumar ta EFCC ta fitar a ranar Juma’a ta hannun mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwujaren, an kama wanda ake tuhuma tare da wasu mutane 25 a wani samame da aka kai da sassafe a wurare daban-daban a Ilorin a ranar Alhamis, 4 ga watan Mayu, 2023.
Wadanda ake zargi da aikata laifukan Intanet sune; Yusuf Ahmed, Abdulazeez Ademola, Sulyman Mustapha, Yekeen Ibrahim, Samuel Adebayo, Raheem Moshood, Badmus Yusuf, Nurudeen Abdulmajeed, Abiodun Ayomide, Samuel Anuoluwapo, Ayodele Samuel, Ramadan Tijani, Soyinka Idris, Abdulhameed Junaid, Bashit Ismail, Temidayo Victor, Pelumi Adeboye , Lekan Oyedepo and Kudus Buhari.
Sauran su ne; Oyedepo Julius, Oyedepo James, Adeboye Pelumi, Akole John, Mustapha Bashir da Solomon Tomiwa.
“Da yake aiki da sahihan bayanan sirri, jami’an sun sake kama wasu da ake zargi da damfara ciki har da mamba mai hidima na kasa, Salaudeen Muhammed da wasu 35.
“Sun hada da Ashaolu Femi Richard, Olabisi David Oluwaseun, Adeyemi Marvelous David, Adekunle Aliyu Adeniyi, Amao Ibrahim Oluwasegun, Fakeye Tolulope Emmanuel, Fawaaz Ajibola, Lawal Adebayo Muritala, Sulaiman Saheed Olayinka, Azeez Ibrahim Olarewaju, Ayoola Emmanuel, Babatunde Oluwatomiwa Peter, Mayomi Olamide Faith, Samuel Mayomi Oluwaseun, Ayanda Samuel Oluwapelumi, Ajayi Mubarak Okikiola, Oke Ibukun Oyebisi, Owolaja Abayomi Oyewole, Taiwo Olatunbosun Apariola da Yusuf Olamilekan Ibrahim.”
Sauran wadanda ake zargin sune; Alufoge Toba Oluwaremilekun, Abiola Asimiyu Lukman, Quwam Lanre Busari, Damola Bello Lateef, Tijani Ridwan Lekan, Adeoye Quadri Olalekan, Folarori Abeeb Oladimeji, Bashit Abiodun Soneye, Adeoye Abdulgafar Olamide, Oladimeji Gabriel Junior, Ayinla Qudus Bashird, Uthman Mustapha, Uthman Mustapha. , Seun Elijah Simon and Taofik Qoweeyu Bosun
“Kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da manyan motoci, nau’ikan wayoyi da kwamfyutoci daban-daban, laya, da dai sauransu. Za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu bayan kammala binciken da ake yi,” in ji hukumar.