Jami’an rundunar shiyyar Enugu na Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) a jiya sun kama wasu mutane 36 da ake zargi da damfarar yanar gizo.
Hukumar ta ce wadanda ake zargin sun aikata zamba ta yanar gizo da suka shafi ‘yan kasashen waje.
Wadanda ake zargin sun hada da: Chukwuma Destiny, Emenalom Precise, Nwaeze Obinna, Ogbonna Monday, Raymond Chigozie, Mmadu Bright, Chigozie Sixtus, Ike Joachim Uchechukwu, Ifeanyi Uzor, Iwuanyanwu Divine, Nwoke Udojah, Patrick Micheal, Chukwu Hillary, Charles Nneji, Nwachukwu Chibueze, Obinna Ajem, Egwu Williams da Samuel Michael.
Sauran sun hada da: Ike Joseph, Ekperi Ikechukwu, Iwwohen Ikechukwu, Joshua Emmanuel, John Dickson, Madu Sixtus, Onyemauche Tochukwu, Chibueze wonderful, Precious Uchenna, Amamasim Bright, Ibeawuchi Obumneke, Ihugba Chikamso, Chima Charles, Christian Mahakwe, Okorie Arinze, Chukwu Kenechukwu , Mahakwe Charles da Chima Fidel.
An kama su ne a Owerri, jihar Imo, biyo bayan wasu sahihan bayanan sirri da ke alakanta su da zamba ta yanar gizo da ake yi wa galibin ‘yan kasashen waje.
Kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun hada da wayoyi da dama, kwamfutar tafi-da-gidanka, fasfo na kasa da kasa, Lexus ES350 daya mai lamba NYCN mai lamba IMO 44, Mercedes Benz GLK daya mai lamba KTU 729 HD da Toyota Camry guda daya mai lamba KTU 720 HL.
Sanarwar da EFCC ta fitar ta ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.