Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, shiyyar Fatakwal, ta kama wasu mutane 26 da ake zargi da damfarar yanar gizo a gidan a Fatakwal, jihar Ribas.
An tattaro cewa an kama su ne biyo bayan sahihan bayanan sirri kan zargin su da hannu a ayyukan da suka shafi intanet.
Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya ce abubuwan da aka kwato daga hannunsu sun hada da nau’ikan wayoyi daban-daban, kwamfutar tafi-da-gidanka da wasu manyan motoci guda shida.
Ya kara da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.