Jami’an rundunar shiyyar Makurdi na Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati, EFCC, sun kama wasu mutane 23 da ake zargi da damfarar yanar gizo.
An kama wadanda ake zargin ne a wani samame da aka kai a garin Makurdi na jihar Benue.
An bayyana sunayensu da David Uvaa, Patrick Adakole, Cyprian Aloo, Michael Anaambe, Okti Clinton, Ibi Raphael, Anaambe George, Msaasha John, Oche Edache, Anaker Terpase, Tanko Japhet da Ayalgo Lorfa.
Sauran sun hada da Success Terzungwe, Suursuter Isaiah, Lawani Peter, Paul Adewa, Jacob Paul, Ibi Shedrack, Iorkosu Michael, Shiedu Leonard, Terseer Mnenge, Ikyorna Raphael da Igba Ngutor.
Hukumar, a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Twitter, ta ce abubuwan da aka kwato daga hannunsu sun hada da wayoyin hannu daban-daban da kuma mota kirar Toyota Corolla guda daya.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kara da cewa wadanda ake zargin sun yi bayanai masu amfani kuma za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.


