Jami’an rundunar shiyyar Uyo na Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati, EFCC, sun kama wasu mutane 17 da ake zargi da damfarar yanar gizo a wurare daban-daban a Uyo, Jihar Akwa Ibom.
An kama wadanda ake zargin ne a yayin wani samame da aka kai bayan wasu rahotannin sirri da ke alakanta wadanda ake zargin da aikata laifuka iri-iri ta yanar gizo.
Hukumar ta tabbatar da kamun ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter.
Kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da; wayoyin hannu, na’urar talabijin, mota kirar Toyota Camry LE, bakar mota kirar Honda da kuma motoci Lexus guda biyu.
“Za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa Kotu da zarar an kammala bincike,” in ji ta.


