Jamiāan hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, reshen jihar Benin a ranar Alhamis, sun kama wasu mutane 26 da ake zargi da damfarar yanar gizo a maboyar su da ke Asaba, jihar Delta.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta bayyana hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter.
Wadanda ake zargin sun hada da āAustin Okolo, Modebe Olisa, Onyemailu Chisom, Igbudy Collins Eloho, Onyema Okwuose, Daniel Idoko Emumena, Chidibele Kelvin, Pius Ikwebe, Azubuike Maxwell Odor, Obaze Justice, Monye Emeka Divine, Okirhienye Oghenetega, Gwamna Anointed. Nebeolisa Obinna.
Sauran sun hada da, Johnson Nnaemeka da Augstine Imunor, Ukazu Henry, Destiny Ikpekpe, Joromi Odoko, Clinton Oletu Emma, Nicholas Brain, Anamali Azuka, Nonye Fimber Dugbele, Nwazi Ebuka, Chmezie Emeka da Onyeje Chuka.
Kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da mota kirar Toyota Camry, motoci kirar Mercedes Benz C300 guda biyu, wayoyin hannu da kwamfyuta.
Hukumar ta kara da cewa nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya


